logo

HAUSA

AU ta yabawa taimakon kasar Sin na yaki da COVID-19 a Afrika

2022-02-04 19:43:40 CMG

AU ta yabawa taimakon kasar Sin na yaki da COVID-19 a Afrika_fororder_0204-AU-COVID-19-Faeza(1)

Kwamshinan lafiya da ayyukan agaji na Tarayyar Afrika AU, Samate Cessouma Minata, ta ce kasar Sin ta rika taimakawa AU da mambobinta, wajen shawo kan annobar COVID-19 tun bayan barkewarta.

Samate Cessouma Minata, ta bayyana haka ne, yayin da take jawabi ga wani taron manema labarai a gefen taron majalisar zartarwar Tarayyar.

Taron ya hada ministocin harkokin wajen kasashen AU da ya gudana a hedkwatarta dake Addis Ababa na Habasha, shi ne irinsa karo na farko tun bayan barkewar annobar.

Kwamshinar ta kara da cewa, Sin ta kasance abokiyar huldar ta musammam da ta taimakawa Afrika yaki da cutar a fadin nahiyar.

Har ila yau, ta ce tana taya Sin murna tare da gode mata, bisa taimakonta ga baki dayan nahiyar tun bayan barkewar annobar, tana mai cewa taimakon na Sin bai tsaya kadai ga tarayyar ba, har ya kai ga mambobinta. (Fa’iza Mustapha)

Faeza