logo

HAUSA

Zambia za ta ci gaba da marawa Sin baya game da zuba jari a ginin tashar samar da taki

2022-02-04 19:41:59 CMG

Zambia za ta ci gaba da marawa Sin baya game da zuba jari a ginin tashar samar da taki_fororder_0204-Zambia-Faeza

Hukumar raya kasar Zambia (ZDA), ta ce za ta ci gaba da marawa kasar Sin baya wajen gina tashar samar da taki a kasar.

Mukaddashin shugaban hukumar, Albert Halwampa, ya jinjinawa ci gaban da aka samu tun bayan da kamfanin United Fertilizer, wanda wani reshe ne na kamfanin Wonderful Group na kasar Sin, ya kaddamar da aikin ginin tashar a watan Nuwamban bara, aikin da zai lakume dala miliyan 300.

Da yake jawabi bayan rangadin aikin ginin tashar a Lusaka, jami’in ya bayyana farin ciki ganin cewa, ba biyan bukatun kasuwar cikin gida kadai tashar za ta yi ba, har ma da duba yuwuwar fitar da takin zuwa ketare. Ya kuma bayyana jin dadin ganin tashar ta dace da kare muhalli.

A cewar kamfanin United Fertilizer, ana sa ran tashar, wadda aka shirya kaddamarwa a hukumance cikin watan Yuli, za ta samar da ton 300,000 na taki a kowacce shekara. (Fa’iza Mustapha)

Faeza