logo

HAUSA

Ministan wajen Sin ya gana da takwaransa na kasar Rasha dake ziyara a kasar

2022-02-04 19:48:01 CMG

Ministan wajen Sin ya gana da takwaransa na kasar Rasha dake ziyara a kasar_fororder_0204-WangYi-Ibrahim

Jiya ne, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a nan birnin Beijing,fadar mulkin kasar Sin, a gabar da suke shirye-shirye a fannin siyasa don ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu.

Wang ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, za su gana ido da ido a yau Juma'a a karon farko cikin fiye da shekaru biyu. Yana mai cewa, babban aikin da zai yi na ganawarsa da Lavrov shi ne, yin shiri na karshe na siyasa, don neman samun bunkasuwar tattalin arziki a kasarsa a ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi

Jami’in na kasar Sin ya bayyana cewa, bisa amincewar shugabannin kasashen biyu, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da kasar Rasha, wajen zurfafa abokantaka da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, da tabbatar da adalci da daidaito a duniya, da samar da karin moriya ga jama'ar kasashen biyu da ma duniya baki daya.

A nasa bangare kuwa, Lavrov ya ce, kasar Rasha ta yaba da kokarin da kasar Sin ke yi, na zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, kuma a shirye Rashan take ta yi aiki tare da kasar Sin, wajen neman karin hadin gwiwa tsakanin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yankin Turai da Asiya (Eurasia), da shawarar ziri daya da hanya daya don fadada moriyar juna.(Ibrahim)

Ibrahim