logo

HAUSA

Xi ya gana da takwaransa na kasar Rasha

2022-02-04 17:25:43 CRI

Xi ya gana da takwaransa na kasar Rasha_fororder_hoto

Da yammacin yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing.

A yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya bayyana cewa, yana son hada kai da shugaba Putin, da ma sauran shugabannin kasashen duniya wajen karfafa ra’ayin Olympics. Kuma, ya yi imanin cewa, ganawarsa da shugaba Putin za ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare kuma, shugaba Putin ya ce, kasar Sin abokiya ce mafi muhimmanci ga kasar Rasha, yana kuma fatan al’ummomin kasar Sin za su cimma gagarumar nasara bisa jagorancin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin.

Wannan shi ne karo na 38 da shugaba Xi ya gana da shugaba Putin tun daga shekarar 2013, da ya kama aikin shugaban kasar Sin. Kuma karo na farko, da suka yi ganawa fuska da fuska bayan barkewar annobar cutar COVID-19.

Bayan ganawar tasu, bangarorin biyu sun fidda sanarwar hadin gwiwa game da dangantakar kasa da kasa cikin sabon zamani da dauwamammen ci gaban duniya. (Maryam)