logo

HAUSA

An Yi Bikin Bude Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Karo Na 24

2022-02-04 21:52:27 CRI

An Yi Bikin Bude Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Karo Na 24_fororder_hoto

A daren yau Jumma’a ne, aka kaddamar da bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu karo na 24 a filin wasannin motsa jiki na kasar Sin dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin, inda ya sanar da bude gasa.

Shugaban kwamitin gasar Olympics na kasa da kasa Thomas Bach, da babban magatakardan MDD Antonio Guterres, da shugaban kasar Rasha Vladimir Vladimirovich Putin, da kuma wasu shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, da shugabanni daga kasashe sama da 30 dake nahiyoyin Turai, Asiya, Afirka, Latin Amurka sun halarci bikin.

Gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing ita ce babbar gasar wasannin motsa jiki da aka gudanar bisa lokacin da aka tsara a karo na farko, tun bayan barkewar annobar cutar COVID-19. ’Yan wasan motsa jiki sama da dubu 3 da suka zo daga kasashe 90 ne za su halarci gasar, kuma, wasannin da za su yi, da kuma lambobin yabo ta zinari da za a bayar, sun kasance mafi yawa a tarihin gasar Olympics ta lokacin hunturu. Kana, a karo na farko, wasu kasashe sun tura ‘yan wasan motsa jiki zuwa gasar Olympics ta lokacin hunturu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)(Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samar da hoto)