logo

HAUSA

Mutane Miliyan 137 Sun Je Yawon Shakatawa A Farkon Kwanaki Uku Na Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin

2022-02-04 15:57:53 CRI

Mutane Miliyan 137 Sun Je Yawon Shakatawa A Farkon Kwanaki Uku Na Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin_fororder_220204-bikin-bazara-ziyara-Maryam-hoto

Alkaluman kididdigar da ma’aikatar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin ta fidda sun nuna cewa, a farkon kwanaki uku na hutun bikin bazara, adadin mutanen da suka tafi yawon shakatawa a yankunan karkara, da filayen wasan kankanra, da wuraren tarihi da dai sauran wurare, ya karu sosai.

Kuma, bayanin ya nuna cewa, mutane miliyan 137 sun tafi yawon shakatawa cikin wadannan kwanaki uku a kasar Sin, adadin da ya kai kashi 71.5 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2019. Kuma, adadin kudaden shiga a fannin yawon shakatawa da aka samar, ya kai RMB yuan biliyan 167.849. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)