logo

HAUSA

ECOWAS za ta tura dakarun kwantar da tarzoma zuwa Guinea Bissau

2022-02-04 19:44:56 CMG

ECOWAS za ta tura dakarun kwantar da tarzoma zuwa Guinea Bissau_fororder_0204-Guinea-Faeza

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afrika, ta yanke shawarar tura dakarun kwantar da tarzoma zuwa kasar Guinea Bissau, domin taimakawa tabbatar da tsaro a kasar, bayan yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a ranar Talata.

Shugaban hukumar ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou, ya bayyana yayin wani taron manema labarai da ya gudana bayan taron shugabannin kasashen kungiyar cewa, ECOWAS ta yanke shawarar tura dakaru zuwa kasar, domin kare demokradiyya da tabbatar da tsaro da zaman lafiya. .

Ya ce irin wannan yunkuri ne ECOWAS ta yi a baya, tun daga shekarar 1994, wajen tabbatar da demokradiyya a kasar da ta fuskanci juyin mulki har sau biyu da yakin basasa da kisan shugaban kasa da sojoji suka yi.

A ranar Laraba ne gwamnatin Guinea Bissau ta tabbatar da mutuwar mutane 11 biyo bayan wani yunkurin juyin mulki da ya faru a kasar a ranar Talata. (Fa’iza Mustapha)

Faeza