logo

HAUSA

Fadar White House ta ce Biden zai kalli wasanni Olympic ta Beijing

2022-02-03 16:38:58 CMG

Fadar White House ta ce Biden zai kalli wasanni Olympic ta Beijing_fororder_0203-Biden-Ahmad~1

Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya shirya tsaf domin kallon gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 dake tafe, kamar yadda Jen Psaki, sakatariyar yada labaran fadar White House ta bayyana.

Psaki ta fadawa ‘yan jaridu yayin jawabi ga manema labarai da aka saba gudanarwa kullum a fadar White House cewa, “hakika, babu tantama, muna cigaba da sa lura tare da bayyana tabbacin da muke dashi ga ‘yan wasanmu na Amurka wadanda zasu fafata a gasannin."

A gobe Juma’a ne za a yi bikin bude gasar wasannin, inda ake sa ran gudanar da gasar tsakanin 2 zuwa 20 ga watan Fabrairu.

Tawagar Amurka tana kumshe da ‘yan wasa 224.

Sarah Hirshland, shugabar kwamitin shirya wasannin Olympic da gasar nakasassu ta kasar Amurka, a watan jiya ta bayyana cewa, wasannin motsa jiki na Olympic suna bayyana kyakkyawar kwarewar bil adama da taimakawa fagen gasar wasanni, kuma gasar Olympic ta Beijing 2022 ba zata kasance mai bambanci ba.(Ahmad)

Ahamd