logo

HAUSA

Xi zai halarci bikin bude gasar Olympic ta hunturu ta Beijing

2022-02-03 16:36:37 CMG

Xi zai halarci bikin bude gasar Olympic ta hunturu ta Beijing_fororder_0203-Xi to Attend-Ahmad

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing 2022, wanda za a gudanar a gobe Juma’a 4 ga watan Fabrairu a babban filin wasa na kasar.

Xi, wanda kuma shine babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban hukumar koli ta sojojin kasar, zai jagoranci kaddamar da bude wasannin.

Babban gidan radiyo da talabijin na kasar CMG zai watsa bikin kai tsaye, kana shafin yanar gizo na xinhuanet.com zai watsa hotuna da rubutattun bayanan bikin kai tsaye.(Ahmad)

Ahmad