logo

HAUSA

Jami’ar AU ta yabawa gudunmawar da Sin ke bayarwa don bunkasa kayayyakin more rayuwa a Afrika

2022-02-03 16:35:27 CMG

Jami’ar AU ta yabawa gudunmawar da Sin ke bayarwa don bunkasa kayayyakin more rayuwa a Afrika_fororder_0203-AU-Ahmad

Kasar Sin ta kasance a matsayin jigo idan ana batun cigaban kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afrika, a cewar Amani Abou-Zeid, kwamishiniyar kayayyakin more rayuwa da makamashi ta kungiyar tarayyar Afrika AU.

Abou-Zeid, ta bayyana hakan ne a taron manema labarai, a gefen taron kolin shugabannin majalisar zartaswar AU, wanda ya tattaro ministocin harkokin wajen kasashen Afrika da aka gudanar a helkwatar AU dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, kuma taron shi ne karo na farko tun bayan barkewar annobar COVID-19.

Tace, “akwai gamayyar kasashe da muke ayyuka tare a fannoni daban daban. Tabbas, kasar Sin ta kasance a matsayin mafi muhimmanci wajen bunkasa cigaban kayayyakin more rayuwa a dukkan kasashen Afrika," ta kara da cewa, “kasar Sin ta kasance a matsayin jigo idan ana batun samar da kayayyakin more rayuwa a Afrika."

Taron shugabannin majalsar kolin na AU na kwanaki biyu, taken taron na bana shine, “Gina muhimmin sauyi a fannin abinci mai gina jiki a nahiyar Afrika: Gaggauta samar da cigaban dan adam, da cigaban zamantakewa, da bunkasar tattalin arziki."

Amani Abou-Zeid, ta kuma zayyana irin rawar da kasar Sin ke takawa wajen tallafawa ajandar AU ta shekaru 50 ta bunkasa cigaban nahiyar Afrika, wato ajandar AU 2063, tana mai cewa, “A bangarenmu na hukumar gudanarwar AU, muna godiya ga irin salon da kasar Sin ta dauka wajen zurfafa hadin gwiwa tare da ba da fifiko ga Afrika da kuma ajandar cigaban nahiyar nan da shekarar 2063."(Ahmad)

Ahmad