Hadin kai wajen gudanar da gasar Olympic zai amfana Sin da duniya baki daya
2022-02-03 16:01:59 CRI
Tun bayan da kasar Sin ta yi nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi a shekarar 2015, kasar Sin ta yi amfani da kwarewar wasannin Olympics na Beijing da sauran kasashe wajen karbar bakuncin gasar, kuma ta shigar da manufar bude kofa ga daukacin tsarin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi. A cikin 'yan shekarun nan, kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing ya zabo kwararru daga kasashen waje 37 tare da gabatar da kwararru da na kasashen waje 207 da za su shiga cikin shirye-shiryen gasar.
A sa'i daya kuma, kasar Sin ta dauki matakin yin hadin gwiwa tare da kungiyoyin wasannin motsa jiki na kasa da kasa, wajen gina filayen wasanni, da kankara da dusar kankara, da shirya bukukuwa, da ba da horo, da kuma samun ci gaba da dama, wadanda suka taimaka ga yin mu'amalar wasannin motsa jiki a tsakanin kasar Sin da sauran kasashen waje yadda ya kamata. Matsayin da Sin take dauka na bude kofarta ga waje ya ingiza gasar da ta zama wani karfin dake habaka bude kofarta ga ketare, bisa wani alkawari ne da Sin ta yi.
Gobe za a bude gasar ta Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing a hukumance. Jama’a daga ko’ina a duniya za su hadu a wannan dandali mai salon bude kofa, ba ma kawai ta zama wani gagarumin biki na wasan motsa jiki ba, har ma za a ga niyyar Sin ta ingiza hadin kan kasa da kasa ta fuskar wasannin motsa jiki da bude kofarta da kuma koyi da juna ta fuskar al’adu. (Amina Xu)