logo

HAUSA

Thomas Bach: Beijing ya shirya tsaf

2022-02-03 20:27:08 CRI

Thomas Bach: Beijing ya shirya tsaf_fororder_src=http___p7.itc.cn_images01_20200521_dadba78cac574d0387a2d1f2e356e39d.png&refer=http___p7.itc

Yayin cikakken zaman taro na IOC karo na 139 da aka bude yau Alhamis, shugaban IOC Thomas Bach ya nuna cewa, yanzu Beijing ya shirya tsaf, inda ake daf da gabatar da gasar Olympics mai cike da amincewa da ban mamaki.

Haka kuma, a yau ne, tawagar sa ido data kunshi wakilan kwamitin shirya wasannin Olympic na 2024 da za a yi a Paris da wakilan kwamiti mai kula da harkokin Olympic na 2026 da za a yi a Milan da jami’an IOC, sun duba yadda ake gudanar da gasannin a dakin wasan motsa jiki na kasar Sin da harkokin da suka shafi ma’aikata, inda suka bayyana cewa, Beijing ya gudanar da aikin shiryawa da kyau, ya kuma zama abin koyi ga sauran kasashen da za su karbi bakuncin gasar nan gaba.(Amina Xu)