logo

HAUSA

Jami'in AU: Dangantakar Sin da Afirka a fannin ilimi, kimiyya da fasaha na samun ci gaba a karkashin tsarin FOCAC

2022-02-03 16:31:13 CMG

Jami'in AU: Dangantakar Sin da Afirka a fannin ilimi, kimiyya da fasaha na samun ci gaba a karkashin tsarin FOCAC_fororder_0203-AU-sin-education-Ibrahim

Mukaddashin shugaban sashin ilimi a bangaren kula da ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire a hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Hambani Masheleni ya bayyana cewa, an kafa hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire ta hanyar babban tsarin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC),

Jami’in na AU, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya kira, a gefen bude taron majalisar zartaswar ta AU jiya Laraba, wanda ya hada ministocin harkokin wajen kasashen Afirka a helkwatar kungiyar AU da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a karon farko, tun bayan barkewar cutar COVID-19.

Masheleni ya ce, hadin gwiwar da kungiyar ke yi da kasar Sin da kuma abubuwan da ake yi a wadannan fannoni, ba shakka suna da yawa. Yana mai cewa, ana yin hadin gwiwa da kasar Sin ta hanyar babban tsarin dandalin FOCAC, wanda zai hada kasar Sin da sauran kasashen Afirka waje guda.(Ibrahim)

Ibrahim