logo

HAUSA

Shugaban Amurka ya aike da gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin

2022-02-02 17:16:41 CMG

Shugaban Amurka ya aike da gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin_fororder_0202-Biden-Ibrahim~1

Jiya ne, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya aike da sakon gaisuwarsa a farkon sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.

Gidauniyar shugaban Amurka na 46, ta wallafa a shafinsa na tiwita cewa, Biden da mai dakinsa ​​Jill sun yi bikin sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin tare da ma'aikatan fadar White House a ranar Litinin, yayin da suke makala hoton da suka dauka a karkashin jajayen fitilun da ke rataye a cikin wani dakin taro.

Biden ya ce, muna aika gaisuwa ga duk wanda ke wannan biki, kuma muna yi muku fatan zaman lafiya, da wadata, da lafiya a shekarar dake tafe

A cikin wani sakon Tiwita na daban, shugaba Biden ya rubuta cewa, yana godiya ga gagarumar gudummawar da Amurkawa ‘yan asalin Asiya da tsibirin fasifik (AAPI) suka bayar ga al'ummarmu,da tattalin arzikinmu, da al'adunmu.

Ita ma mataimakin shugaban kasar Amurka Kamala Harris, ta wallafa wani gajeren bidiyo a ranar Talata domin murnar sabuwar shekarar gargajiyar ta kasar Sin.

Tana mai cewa, ga mutane a dukkan fadin duniya da kuma a nan gida Amurka, sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa, lokaci ne na farin ciki da kasancewa tare da dangi da abokai.(Ibrahim)

Ibrahim