logo

HAUSA

Guterres ya nada dan Najeriya a matsayin kwamandan UNISFA a Abyei

2022-02-02 17:15:16 CMG

Guterres ya nada dan Najeriya a matsayin kwamandan UNISFA a Abyei_fororder_0202-UN-Ibrahim~1

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, a ranar Talata ya sanar da nadin manjo Janar Benjamin Olufemi Sawyerr dan kasar Najeriya, a matsayin kwamandan rundunar tsaro ta MDD ta wucin gadi a yankin Abyei (UNISFA).

Shi dai yankin Abyei, yanki ne da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kansa.

Sawyerr ya maye manjo Janar Kefyalew Amde Tessema dan kasar Habasha, wanda babban sakataren ya nuna godiya ga sadaukarwa, da hidima da kuma kyakkyawan jagoranci da ya nuna a lokacin nada shi jagoran UNISFA, kamar yadda ofishin yada labarai na babban sakataren ya bayyana.

Sawyerr dai ya shafe shekaru sama da 34 yana aiki a rundunar sojin Najeriya, ciki har da daraktan yada labarai na rundunar tsaron Najeriya tun daga shekarar 2021.

Ya samu digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da ke Najeriya, sannan ya yi digiri na biyu a fannin tsaro da dabaru a Jami’ar Madras da ke kasar Indiya.(Ibrahim)

Ibrahim