logo

HAUSA

Shugaba Xi ya amsa wasikar da wasu magadan garin Amurka suka rubuta masa

2022-02-02 20:04:16 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikun da magajin garin Tacoma Victoria Woodards, da magajin garin Steilacoom Dick Muri suka aike masa. Cikin wasikar martanin da ya gabatar wa magadan garin biyu, shugaba Xi ya ce, gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing dake tafe, lokaci ne na farin ciki ga Sinawa, kuma gasar wasanni ce da za ta kayatar da sassan kasa da kasa. Ya ce da tallafin daukacin al’ummar Sin, da sauran sassan kasa da kasa, za a gudanar da gasa mai sauki, mai tsaro da kayatarwa.

A baya bayan nan, magadan garuruwan biyu dake karkashin birnin Washington na Amurka, sun rubutawa shugaba Xi Jinping wasiku, na taya shugaban na Sin da al’ummar Sin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kalandar kasar Sin, suna masu fatan gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, za ta gudana lami lafiya.   (Saminu)

Saminu