logo

HAUSA

Shugabannin kasashen ketare sun aikewa Xi Jinping sakwanni fatan cimma nasarar gasar Olympics ta lokacin hunturu

2022-02-02 20:20:44 CRI

Shugabannin kasashen ketare sun aikewa Xi Jinping sakwanni fatan cimma nasarar gasar Olympics ta lokacin hunturu_fororder_220202-shugabanni-sako-Maryam3-hoto

Kwanan baya, shugabannin kasashen duniya da dama, da wasu shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, sun aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping sakwannin fatan alheri ga kasar Sin, suna masu fatan za a cimma nasarar gudanarwar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu, ga kuma gasar Olympics ta lokacin hunturu ta nakasassu.

Cikin sakonsa, shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya bayyana cewa, kasar Sin ta gina dakunan wasannin motsa jiki mafiya inganci a duniya, kuma ‘yan wasan kasashen duniya suna sa ran yin gasa a birnin Beijing. Daga nan sai ya yi fatan alheri ga gwamnati da al’ummomin kasar Sin, domin cimma nasarar gudanar da gasar, ta yadda jama’ar kasashen duniya za su nishadantuwa da ita a birnin Beijing.

Ita ma shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, cewa ta yi tana fatan kasar Sin za ta cimma nasarar gudanar da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing yadda ya kamata. (Maryam)