logo

HAUSA

Amincewa da rayuwa tare da Omicron mataki ne da kimiyya ba za ta amince da shi ba

2022-02-01 19:24:25 CMG

Amincewa da rayuwa tare da Omicron mataki ne da kimiyya ba za ta amince da shi ba_fororder_0201-Omicron-Saminu~1

Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore, ta wallafa wata makala mai taken “Amincewa rayuwa tare da Omicron, mataki ne da kimiyya ba za ta amince da shi ba, kuma hakan yana tattare da hadari”. A cikin makalar, jaridar wadda ake wallafawa da Sinanci, ta ce duniya ta ga yadda ake aiwatar da manufofi guda 2 mabanbanta, wato daukar tsauraran matakan yaki da nau’in cutar COVID-19 na Omicron, da kuma rungumar rayuwa tare da cutar.

Ta ce daukar tsauraran matakan yaki da Omicron, shi ne salon da kasar Sin ke bi don yaki da cutar, inda a cikin shekaru 2, Sin ta yi aiki tukuru wajen yaki da annobar, ta kuma cimma manyan nasarori da suka baiwa duniya mamaki.

A daya hannun kuma, wasu sassa sun rungumi rayuwa tare da wannan cuta ta COVID-19, matakin da ko shakka ba bu, ba zai samu amincewar ilimin kimiyya ba, yana kuma cike da hadari, kamar yadda jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta wallafa.     (Saminu)

Saminu