logo

HAUSA

Bincike: Riga-kafin COVID-19 na kasar Sin da aka fi amfani dasu suna da tasirin yakar nau’in Delta

2022-02-01 19:10:22 CMG

Bincike: Riga-kafin COVID-19 na kasar Sin da aka fi amfani dasu suna da tasirin yakar nau’in Delta_fororder_0201-allura-Ahmad~1

Wani binciken da aka gudanar daga bangarorin majinyata daban daban ya nuna cewa, riga-kafin annobar COVID-19 na kasar guda biyu da aka fi amfani da su, wadanda kamfanonin hada magunguna na Sinovac da Sinopharm suka samar dasu, an gano suna da matukar inganci wajen yaki da cutar COVID-19 nau’in Delta.

Cikin takardar binciken da gamayyar manazarta suka wallafa, ta nuna cewa, riga-kafin biyu suna da ingantacin da ya kai kashi 52 bisa 100 wajen yakar cutar nau’in Delta da kuma kashi 60 bisa 100 na magance nuna alamomin kamuwa da cutar.

Binciken bai samar da isassun alkaluman bayanai da zasu nuna ingancin riga-kafin biyu daga mabanbantan bangarori ko kuma rukunin shekaru ba, kwararrun masu bincike daga hukumar yaki da cutar na cikin gida da kuma wasu jami’oi biyu na kasar Sin sun bayyana a cikin takardar da aka wallafa a sashen bayanan tarihi na mujallar kiwon lafiyar al’umma.

Alkaluman sun ta’allaka ne bisa ga binciken da aka gudanar kan masu dauke da kwayar cutar sama da 100, da kuma sama da mutane 10,000 da suke yi mu’amala ta kusa da mutanen da suka kamu da cutar nau’in Delta a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin a watannin Mayu da kuma Yunin shekarar bara.

Haka zalika, binciken ya gano riga-kafin biyu suna da ingancin da ya kai kashi 78 bisa 100 wajen warkar da masu fama da cutar, sannan suna da ingancin da ya kai kashi 100% na magance yanayi mai tsanani na kamuwa da cutar ta COVID-19.(Ahmad)

Ahmad