logo

HAUSA

Kudaden shigar sashen kera manhajoji na Sin ya karu a shekarar 2021

2022-02-01 19:19:12 CMG

Kudaden shigar sashen kera manhajoji na Sin ya karu a shekarar 2021_fororder_0201-software-Saminu~1

Kudaden shigar sashen kera manhajojin na’ura mai kwakwalwa, da harkar fasahar sadarwa na Sin, ya samu karuwa a shekarar 2021 da ta gabata, inda ribar da sashen ke samu ta karu a shekarar ta bara.

A cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar MIIT, sashen na da jimillar kamfanoni sama da 40,000, wadanda harajin su na shekara guda ya haura kudin Sin yuan miliyan 5, kwatankwacin dalar Amurka 784,363. Yayin da jimillar harajin su na shekara guda ya kai kusan yuan tiriliyan 9.5, adadin da ya karu da kaso 17.7 bisa dari a shekara guda.

Alkaluman MIIT sun nuna cewa, sashen hidimomin fasahar sadarwa na Sin, ya samu bunkasa sosai a bara, inda harajin sashen ya daga da kaso 20 bisa dari a shekara guda, da darajar sama da yuan tiriliyan 6, adadin da kuma ya kai kaso 2.3 bisa dari, sama da matsakaicin karuwar mizanin sauran sassan dake fannin.

MIIT ta kuma bayyana cewa, sashen kirar manhajoji na Sin ya samu ribar da jimillarta ta karu da kaso 7.6 bisa dari a shekara guda, wato kusan ribar yuan tiriliyan 1.19 ke nan a shekarar ta bara.    (Saminu)

Saminu