logo

HAUSA

BOCOG: Shirye shiryen gasar motsa jiki ta Beijing 2022 sun kammala

2022-02-01 20:17:43 CMG

BOCOG: Shirye shiryen gasar motsa jiki ta Beijing 2022 sun kammala_fororder_0201-Olympics-Ahmad~1

Mashirya gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 sun sanar cewa, dukkan shirye shiryen gasar sun kammala inda ake sa ran bude gasar a ranar 4 ga watan Fabrairu.

Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing wato (BOCOG), ya gudanar da taron manema labarai mai taken “Wasannin motsa jiki na hunturu, wasanni, da al’adu" wanda aka gudanar a babbar cibiyar ‘yan jaridu ta Beijing 2022 a ranar Litinin, inda aka sake yin alkawarin cewa kasar Sin zata jagoranci wannan zagayen wasannin “cikin tsanaki, da tsaro, da kuma nuna bajinta.”

Zhao Weidong, kakakin kwamitin BOCOG, yace, kasancewar gasar wasannin ta zo a daidai lokaci guda da bikin bazarar kasar Sin, kasar ta mayar bukukuwan tamkar wata kyautar sabuwar shekara wacce zata gabatarwa duniya.(Ahmad)

Ahmad