logo

HAUSA

Zazzabin Lassa ya kashe mutane 32 a Najeriya

2022-02-01 19:13:46 CMG

Zazzabin Lassa ya kashe mutane 32 a Najeriya_fororder_0201-Nigeria-Ahmad~1

Hukumomi sun bada rahoto cewa, cutar zazzabin Lassa da ta barke a Najeriya ta yi sanadiyyar kashe rayuka akalla 32 tun bayan barkewar cutar a farkon wannan shekarar.

A wasu bayanai game da halin da ake ciki wanda hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasar (NCDC) ta fitar sun nuna cewa, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 74, yayin da jimillar mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ya kai 759 a tsakanin wannan wa’adi.

A ranar 26 ga watan Janairu, hukumomin lafiyar kasar sun bayyana cewa, sun sake kaddamar da shirin ayyukan gaggawa na yaki da cutar zazzabin Lassa a duk fadin kasar domin dakile barkewar annobar a baya bayan nan.

Hukumar NCDC tace, a shirye take ta tallafawa tawagar hukumomin lafiya na jahohin kasar domin rage tasirin barnar annobar.

Cutar zazzabin Lassa cuta ce dake saurin yaduwa wacce kwayar cutar Lassa ke haifar da ita. Ana samun yaduwar cutar a Najeriya a kusan duk shekara, sai dai an fi samun adadi mafi yawa a lokacin rani.

A cewar NCDC, cutar ta kashe akalla mutane 80 a Najeriya a shekarar da ta gabata.(Ahmad)

Ahmad