logo

HAUSA

An kamalla bikin murnar shekarar Damisa ta kalandar gargajiya ta kasar Sin lami lafiya

2022-02-01 16:30:29 CRI

An kamalla bikin murnar shekarar Damisa ta kalandar gargajiya ta kasar Sin lami lafiya_fororder_微信图片_20220201162741

An kamalla bikin murnar shekarar Damisa ta kalandar gargajiya ta kasar Sin lami lafiya_fororder_微信图片_20220201162746

An kamalla bikin murnar shekarar Damisa ta kalandar gargajiya ta kasar Sin lami lafiya_fororder_微信图片_20220201162750

Da misali karfe 8 na daren jiya Litinin, aka gabatar da bikin murnar shekarar Damisa ta kalandar gargajiya ta kasar Sin.

An gabatar da wannan biki ta amfani da fasahar zamani ta XR da AR a kafofin talabijin, da dai sauran fasahohi da masu kallo suke iya morewa, a bikin da aka watsa ta kafofin kwamfuta dake iya nuna hotuna kan da’ira 720. Wanda hakan ya nishadantar da masu kallo matuka. Bikin dai na samun karbuwa matuka daga masu kallo, da kafofin yada labarai na ketare, wanda ganinsu bikin ke kara samun nasara sosai.

Bisa alkaluman da aka bayar, ya zuwa karfe 12 na tsakar daren jiya, yawan mutanen da suka kalli bikin ya kai kaso 21.93% na daukacin al’ummar Sinawa. Kana an kalli bikin ta yanar gizo sau biliyan 4.932, adadin da ya karu matuka bisa na makamancin lokaci na bara.

Masu bibiyar bikin na kara nuna gamsuwa sosai. Kuma kafofin yada labarai fiye da 600 daga kasashen Amurka, da Canada, da Faransa, da Italiya, da Rasha, da Japan, da Brazil, da Austrilia, da Indiya, da UAE, da Singapore, da Afrika ta kudu, da dai sauransu da jimillar su ta kai 170, sun gabatar da wannan biki kai tsaye, kuma yawan mutanen da suka kalli biki ta CNTV da CGTN, sun zarce sau miliyan 35.24, adadin da ya karu da miliyan 16.58, bisa na makamancin lokaci na bara. (Amina Xu)