logo

HAUSA

Liyafar bikin bazara mai tarihin shekaru 40

2022-01-31 20:16:35 CRI

Liyafar Bikin bazara da babbar kafar yada labarai ta CMG ta shirya tana da tarihin shekaru 40, wadda ta kasance liyafar da tafi samun yawan masu kallo a duniya.

Liyafar bikin bazara mai tarihin shekaru 40_fororder_A

A yau, jajibirin sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya, Sinawa sama da miliyan dari daya a duniya suna nishadantuwa da shirye-shiryen liyafar bikin bazara.

Liyafar bikin bazara mai tarihin shekaru 40_fororder_B

A bana, ana gabatar da liyafar ta hanyoyin talabijin da shafin intanet na CMG, a sa’i daya kuma, za a gabatar da shirye-shiryen liyafar ga kasashe da yankuna sama da 170 ta babban gidan talabijin na kasa da kasa na kasar Sin wato CGTN da shafunan intanet na harsuna iri-iri, domin yi wa al’ummomin kasa da kasa fatan alheri. (Maryam)