logo

HAUSA

Shugban kasar Sin da takwaransa na Malta sun aikewa juna sakon murnar cika shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen su

2022-01-31 15:54:39 CRI

Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Malta George Vella, sun aikewa juna sakon murnar cika shekaru 50, da kafuwar dangantakar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Cikin sakon sa, Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 50 da suka gabata, Sin da Malta sun taimakawa juna, sun kuma nuna goyon baya ga juna a harkokin dake janyo hankulansu.

Yanzu haka, ana ci gaba da zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, inda suke hada kai domin yaki da annobar cutar COVID-19, ana kuma samu sakamako masu kyau, lamarin da ya nuna zumunci mai zurfi dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma, ya ce yana son yi hadin gwiwa da shugaban kasar Malta, domin ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da habaka hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, ta yadda za a samu karin sakamako masu kyau, da kuma tallafawa al’ummomin kasashen biyu yadda ya kamata.

A nasa bangare kuwa, shugaba Vella ya ce, bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Malta, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba da bunkasa yadda ya kamata, inda aka cimma sakamako da dama, wadanda suka ba da tallafi ga al’ummomin kasashen biyu. A nan gaba kuma, kasar Malta za ta ci gaba da nuna goyon baya kan hadin gwiwar dake tsakanin kungiyar tarayyar kasashen Turai da kasar Sin, da kuma samar da Karin damammaki ga bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu. (Maryam)