logo

HAUSA

Sinawa Na Kallon Liyafar Bikin Bazara Tare Domin Maraba Da Zuwan Sabuwar Shekarar Damisa

2022-01-31 21:23:10 CRI

Sinawa Na Kallon Liyafar Bikin Bazara Tare Domin Maraba Da Zuwan Sabuwar Shekarar Damisa_fororder_220131-liyafar bikin bazara-Maryam-hoto

Yau Ranar 31 ga watan Janairu ita ce jajibirin sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya. A yanzu haka, Sinawa sama da miliyan dari daya a duniya suna nishadantuwa da shirye-shiryen liyafar bikin bazara da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG ke gabatarwa, domin maraba da zuwan sabuwar shekarar Damisa.

Tun daga shekarar 1983, a kowace shekara, babbar kafar yada labarai ta CMG ta kan gabatar da liyafar bikin bazara a jajibirin sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)