logo

HAUSA

Beijing ta gina dandalin musayar al’adu da fahimtar juna a 2022

2022-01-31 16:52:06 CMG

Beijing ta gina dandalin musayar al’adu da fahimtar juna a 2022_fororder_0131-SCO-Faeza

Sakatare Janar na kungiyar hadin kai ta Shanghai (SCO), Zhang Ming, ya ce wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, ba dandalin takara kadai ya bude tsakanin ‘yan wasan kasa da kasa ba, har ma da dandalin musayar al’adu da fahimtar juna.

Zhang Ming ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Xinhua, gabanin bude wasanni na Beijing na 2022, wadda kasashe 12 na kungiyar za su halarci bikin kaddamarwar da za a yi ranar 4 ga wata, a babban filin wasa na kasar Sin.

A cewarsa, bisa ruhin kungiyar SCO ta mutuntawa da moriyar juna da daidaito da tuntuba, tare da girmama bambamcin al’adu, da neman ci gaba na bai daya, kasashe mambobin kungiyar sun yi kira da a kaucewa siyasantar da wasannin tare da jaddada bukatar kara raya wasannin Olympics da na Paralympic ta nakasassu.

Har ila yau, kungiyar SCO ta yi ammana wasannin biyu na Olympics da ya hada da na nakasassu, za su karfafa abota da fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin kasashe. (Fa’iza Mustapha)

Faeza