logo

HAUSA

An yi bikin mika gaisuwar bikin bazara na majalisar gudanarwar kasar Sin

2022-01-30 17:37:18 CRI

Kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar Sin sun yi bikin nuna gaisuwa domin bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin na shekarar 2022 a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing a yau da safe, inda babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a shekarar sa bisa kalandar gargajiyar kasar Sin da za ta kare, Sin tana matsayin kan gaba a duniya a fannonin bunkasar tattalin arziki da dakile yaduwar cutar COVID-19, da taka muhimmin mataki na kafa sabon tarihi a fannin bunkasuwa, da samun sabbin nasarori kan samun bunkasuwa mai inganci. Kana Sin tana gaggauta raya sha’anin kimiyya da fasaha, da yin kokarin ci gaba da bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, da kiyaye tabbatar da zaman rayuwar jama’a, da kiyaye muhallin halittu, da aiwatar da ayyukan daidaita yawan gurbatacciyar iska da ake fitarwa ta hanyoyin shuka itatuwa, da rage fitar da gurbatar iska da sauransu, da raya aikin kiyaye tsaron kasa da sojoji, da kwantar da kura a yankin Hong Kong, da yaki da ‘yan aware, da ci gaba da aiwatar da manufofin diplomasiyya masu alamar kasar Sin, da tabbatar da zaman lafiya a kasar, ta hakan za a bude sabon shafi a lokacin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14.

Xi Jinping ya jaddada cewa, abu mafi jin dadi a duniya shi ne yin kokari domin neman zaman rayuwa mai dadi ga jama’a. Koda yake, ana samun babban sauyi da tinkarar kalubale a duniya, amma membobin jam’iyyar kwaminis ta Sin suna ci gaba da bin tunanin jam’iyyar, da tunawa da fasahohin da aka samu a lokacin da, da yin hangen nesa, da yin hadin kai da juna da yin kokari tare don sa kaimi ga raya al’ummar kasar Sin zuwa sabon matsayi. (Zainab)