logo

HAUSA

Manyan shugabannin kasa da kasa da jami’an MDD suna fatan Sin za ta gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu cikin nasara

2022-01-30 17:38:02 CRI

Yayin da ake dab da bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, manyan shugabannin kasashen Afirka ta Tsakiya, da Kenya, da Tunisia, da Sudan ta Kudu da sauran kasashen duniya da jami’an MDD suna fatan Sin za ta gudanar da gasar cikin nasara.

Shugaban kasar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya bayar da wata sanarwar cewa, gasar wasannin Olympics gasa ce ta duk dan Adam, bai kamata a siyasantar da ita ba.

Ministan harkokin matasa da wasannin motsa jiki na Sudan ta Kudu ya bayyana cewa, sha’anin wasannin motsa jiki na kasar Sin da aka raya yana da alfanu matuka, kuma tushe ne na samun damar daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu, da kuma gudanar da gasar cikin nasara, ya yi imanin cewa, babu shakka za a gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing cikin nasara. (Zainab)