logo

HAUSA

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa: Za’a gayyaci masu kallo don halartar gasar Olympics a nan gaba

2022-01-29 16:56:17 CRI

Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa: Za’a gayyaci masu kallo don halartar gasar Olympics a nan gaba_fororder_11

Za’a kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin sanyi a Beijing a ranar 4 ga watan Fabrairun bana. A yayin da yake zantawa da ‘yan jaridun babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, Thomas Bach ya bayyana cewa, gasar bana a Beijing za ta bude sabon babi ga wasannin dusar kankara na duniya.

Mista Bach ya kuma bayyana cewa, a gasannin Olympics na nan gaba, ba kallo kawai ‘yan kallo za su yi ba, za’a gayyace su don su halarta.

Game da yadda za’a fahimci babban taken gasar ta bana da ake kira “Together For A Shared Future”, wato “Mu Gudu Tare Mu Tsira Tare”, Bach ya ce, taken ya bayyana ma’anar kara hada kai, wanda ke nunawa jama’a muhimmancin zama tsintsiya madaurinki daya, da daukar nauyi kafada da kafada, ta yadda za’a cimma nasara. (Murtala Zhang)