logo

HAUSA

Kwamitin wasannin Olympic na kasar Gabon na fatan wasannin Beijing za su gudana cikin nasara

2022-01-29 16:58:37 CRI

Kwamitin wasannin Olympic na kasar Gabon na fatan wasannin Beijing za su gudana cikin nasara_fororder_241f95cad1c8a7861971a5e324c1043472cf50d2 (1)

Kwamitin shirya wasannin Olympics na Gabon, ya yi wa wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, fatan samun nasara.

Cikin wata sanarwar da aka fitar jiya, shugaban kwamitin Leon Folquet, ya ce kwamitin na fatan wasannin na Beijing, za su gudana cikin nasara kamar wasannin Olympics na lokacin zafi na Beijing na shekarar 2008, yana mai jinjinawa kokarin Sin na shirya manyan wasanni.

Da yake bayyana wasannin lokacin zafi na Beijing na 2008 a matsayin wadanda suka samu gagarumar nasara, Leon Folquet, ya ce Sin ta shirya gabatar da wasannin na hunturu cikin aminci da sauki da burgewa, wadanda za su taka muhimmiyar rawa wajen hada kan duniya.

Ya kara da cewa, kasashen biyu, wato Sin da Gabon, sun dade suna hadin gwiwa a bangaren wasanni, yana mai yabawa ginin filayen wasanni daban-daban da kamfanonin Sin suka yi a kasar, wadanda suka ba ta damar karbar bakuncin gasannin cin kofin nahiyar Afrika har sau 2. (Fa’iza Mustapha)