logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya gabatar da jawabin taya murnar sabuwar shekarar Sinawa

2022-01-29 17:08:51 CRI

Sakatare Janar na MDD ya gabatar da jawabin taya murnar sabuwar shekarar Sinawa_fororder_QQ截图20220129170829

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a jiya, albarkacin sabuwar shekarar gargajiya bisa kalandar kasar Sin, inda ya taya Sinawa a fadin duniya murnar shiga sabuwar shekarar Damisa, tare kuma da fatan samun nasarar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing.

A cewarsa, Damisa na alamta karfi da kuzari da juriya, wadanda suka kasance dabi’un da ake bukata yayin da ake fuskantar kalubalen da ba a taba gamuwa da su ba.

Antonio Guterres, ya kuma yabawa kasar Sin da al’ummarta, bisa gudunmuwarsu ga tsarin huldar kasa da kasa da ma MDD. Yana mai cewa, ya zama wajibi al’ummun kasashe daban-daban su hada hannu domin farfadowar al’amura tare da gina kyakkyawar makoma.

Har ila yau, ya ce zai halarci bikin bude wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing. Yana mai cewa, ruhin wasannin alama ce ta hadin kan bil adama. Kuma yana sa ran za a kammala su cikin aminci da nasara. (Fa’iza Mustapha)