logo

HAUSA

Sin:Matakin Amurka na soke lasisin Unicom na yin aiki a Amurka ya saba dokokin kasuwanci na kasa da kasa

2022-01-28 21:22:05 CRI

Sin:Matakin Amurka na soke lasisin Unicom na yin aiki a Amurka ya saba dokokin kasuwanci na kasa da kasa_fororder_641 (1)

Dangane da soke lasisin kamfanin sadarwa na Unicom na kasar Sin da gwamnatin Amurka ta yi, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, hakan ya yi matukar saba dokokin cinikayyar kasa da kasa. Kuma Kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye hakki da muradun kamfanonin kasarta.

Rahotanni na cewa, gwamnatin Amurka ta sanya kamfanin Unicom da ke Amurka a cikin jerin kamfanonin da a cewarta wai ba sa bisa doka, ta hanyar fakewa da dalilai na "tsaron kasa" tare da dakatar da izinin kamfanin na yin kasuwanci a Amurka.