logo

HAUSA

An bude unguwanin gasar Olympic ta Beijing 2022 a hukumance

2022-01-28 11:39:08 CRI

An bude unguwanin gasar Olympic ta Beijing 2022 a hukumance_fororder_0128-Olympic Villages-Ahmad

A jiya Alhamis, an bude unguwannin gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi ta Beijing 2022 dake kwaryar birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a gundumar Yanqing, da birnin Zhangjiakou na lardin Hebei, an bude kofofinsu a hukumance ga ’yan wasa da tawagar jami’an gudanar da gasar wasannin.

Zhang Guannan, mamban tawagar gudanarwar unguwannin wasannin  Olympic na Beijing, ya ce, unguwannin sun tanadi muhalin zama ga ’yan wasa kusan 1,000 da tawagar jami’ai daga kasashen duniya 44 da shiyyoyi.

Ya kara da cewa, baya ga tanadin ingantattun hidimomin samar da gidajen kwana, kauyen yana kuma da wuraren motsa jiki, da wuraren shakawa, da cibiyoyin kiwon lafiya, domin biyan bukatun ’yan wasa da jami’an. An tanadi nau’ikan abinci 678 domin biyan bukatun mahalartan da kuma wasu zabi na musamman ga sabuwar shekarar Sinawa dake shirin kamawa.

Juan Antonio Samaranch Jr., shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa na hukumar shirya gasar wasannin motsa jiki ta lokacin sanyi ta Beijing 2022, ya nuna yabo game da ingantattun kayayyakin da aka tanada a lokacin da ya ziyarci unguwa, ya kara da cewa, ’yan wasan sun yi babbar nasara game da gudanar da wasannin na Beijing 2022 a cikin kyakkyawan yanayi kuma a yanayi mafi inganci da tsaro. (Ahmad)