logo

HAUSA

An bude taron farko na dandalin kirkire-kirkire a fannin kafafen yada labarai na duniya

2022-01-27 11:25:04 CRI

Jiya Laraba 26 ga wata, aka bude taron farko na dandalin kirkire-kirkire a fannin kafafen yada labarai na duniya a birnin Beijing.

Taron mai taken “Raba ruhin wasannin Olympics na lokacin sanyi ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha” ya samu halartar shugabannin kafofin watsa labarai, da kungiyoyin duniya guda 145 daga kasashe 78, ya kuma gudana ne ta bidiyo.

An bude taron farko na dandalin kirkire-kirkire a fannin kafafen yada labarai na duniya_fororder_巴赫

Shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na duniya Thomas Bach, ya taya murnar kira taron, inda ya nuna cewa, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya samu nasarar shirya taro ta hanyar kirkire-kirkire, bayan da ya haye dimbin wahalhalu.

An bude taron farko na dandalin kirkire-kirkire a fannin kafafen yada labarai na duniya_fororder_慎海雄

A nasa bangaren, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, wasikar murnar da Shugaba Xi Jinping ya aike wa jagorancin CMG, ya taimakawa gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da ma wasannin motsa jiki na Olympics bisa babban taken dandalin, sa’an nan ya sa rai ga muhimmiyar rawar da kafofin watsa labarai ke takawa.

Wasu shugabannin kafofin watsa labarai na duniya sun ba da jawabai ta bidiyo, inda Oleg Dobrodeyev, shugaban gidan rediyo da talibijin na kasar Rasha ya ce, yana sa ran ganin sabbin fasahohi da kirkire-kirkire da CMG za su amfani da su wajen watsa labarai a yayin gasar wasannin Olympics din na lokacin sanyi ta Beijing, wadanda a ganinsa, za su taimaka wa duniya wajen kara jin dadin kallon gasannin.

A nata bangaren kuwa, shugabar kamfanin dillancin labarai na AP na Amurka Daisy Veerasingham ta bayyana cewa, fasahohin zamani na takawa muhimmiyar rawa, ta yadda kafofin watsa labarai ke samar da labaran bidiyon na gari, ta hanyar yin kirkire-kirkire. (Kande Gao)