logo

HAUSA

Liyafar bikin bazara na shekara ta 2022 za ta jawo hankalin jama’a sosai

2022-01-27 19:29:29 CRI

Liyafar bikin bazara na shekara ta 2022 za ta jawo hankalin jama’a sosai_fororder_20220127180404110

Yau Alhamis an yi taron manema labarai game da liyafar bikin bazara ta shekara ta 2022 da babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG zai shirya, inda aka bayyana wasu abubuwan da za su jawo hankalin jama’a a gagarumin bikin.

Za’a yi amfani da fasahohin zamani da dama don gudanar da bikin na bana, musamman karkashin babbar manufar amfani da fasahohin sadarwar zamani na 5G+4K/8K+AI, dake zama wani babban dandalin dake nuna yadda ake yin kirkire-kirkire ga harkokin watsa labarai na rukunin CMG.

Liyafar bikin bazara ta bana, wato bikin murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, za ta mayar da hankali ne kan babban taken nuna farin ciki da samar da alheri, da hada al’adu da fasahohin zamani tare, da gabatar da shirye-shiryen dake bayyana ainihin rayuwar al’umma, ta yadda za’a nuna al’adun dake tattare da bikin bazara na kasar Sin na haduwar iyali da hadin-kan al’umma. (Murtala Zhang)