logo

HAUSA

Shugaba Xi ya ziyarci mutanen da mummunan bala’in ambaliyar ruwa ya ritsa da su a lardin Shanxi

2022-01-27 19:04:00 CRI

Shugaba Xi ya ziyarci mutanen da mummunan bala’in ambaliyar ruwa ya ritsa da su a lardin Shanxi_fororder_eac4b74543a98226960728ed2f1772084890eb51

A gabannin bikin murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al’ummar kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya ziyarci kauyen Fengnanyuan dake garin Shizhuang na birnin Huozhou na lardin Shanxi, a wani kokari na kara fahimtar yadda ake gudanar da ayyukan sake gina wurin bayan abkuwar mummunar ambaliyar ruwa a watan Oktobar bara. Shugaba Xi ya ce, ya zo ne don ganewa idanunsa tasirin da bala’in ya haifar ga rayuwar mazauna wurin. Duk da cewa bala’in ya yi muni, amma sakamakon kulawar jam’iyyar kwaminis gami da gwamnati, mazauna wurin sun himmatu wajen gudanar da ayyukan sake gina wurin da farfado da sana’ar noma a lokacin kaka da na hunturu, abun da ya kwantar da hankalinsa sosai. Shugaba Xi ya kuma yi musu barka da shiga sabuwar shekara.

Kauyen Fengnanyuan da shugaba Xi ya ziyarta, daya ne daga cikin kauyukan da bala’in ruwan sama mai karfi ya fi yi wa muni a watan Oktobar bara. Bayan abkuwar bala’in, an fara gudanar da aikin sake gina wurin ba tare da bata lokaci ba, kuma dukkan mazauna wurin sun koma sabbin gidajen da aka sake ginawa. (Murtala Zhang)