Xi ya mika gaisuwar bikin bazara ga dukkan Sinawa yayin ziyararsa a Shanxi
2022-01-27 21:35:40 CRI
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika gaisuwar bikin bazara ga dukkan al’ummar kasar Sin a ziyarar da ya kai lardin Shanxi da ke arewacin kasar Sin daga ranar Laraba zuwa yau Alhamis.
Xi, ya yi fatan alheri ga al’ummar Sinawa na dukkan kabilu, da 'yan uwa mazauna yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan, da Sinawa dake kasashen waje, da koshin lafiya da jin dadi a cikin shekarar Damisa, da wadata da karfi ga kasa baki daya.