logo

HAUSA

Kasa da kasa na sa ran alheri game da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing

2022-01-27 20:49:18 CRI

Kasa da kasa na sa ran alheri game da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing_fororder_1128307552_16432836778111n

Yayin da mako guda ya rage a fara gasar wasannin motsa jiki na Olympics na lokacin hunturu a Beijing, a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana cewa, yayin da gasar ke karatowa, kasashen duniya na kara nuna fatan alheri da goyon-baya na ganin an gudanar da gasar cikin nasara.

Zhao ya ce, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na duniya Thomas Bach ya jinjinawa kasar Sin, saboda kwarewa da kudiri gami da kuzarinta, inda ya ce akwai wasu kasashen da a karon farko suka turo tawagogi Beijing don halartar gasar, abun da ya shaida cewa, gasar na samun goyon-baya da amincewa daga kasa da kasa. Baya ga haka, shugabanni gami da manyan jami’an kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasashen Rasha da Sifaniya da Argentina da Laos da Najeriya, sun bayyana goyon-bayansu ga gasar, da sake jaddada nuna adawa da siyasantar da wasannin motsa jiki.

Zhao ya kuma nanata cewa, daga shekara ta 2008 zuwa 2022, har yanzu kasar Sin, musamman Beijing, bai sauya sha’awarsa ta maraba da nuna sahihanci ga baki daga kasashe daban-daban ba. (Murtala Zhang)