logo

HAUSA

Najeriya: An kaddamar da cibiyar ko ta kwana domin dakile bazuwar zazzabin Lassa

2022-01-27 09:55:57 CRI

Najeriya: An kaddamar da cibiyar ko ta kwana domin dakile bazuwar zazzabin Lassa_fororder_220127saminu-Nigeria

Hukumomin lafiya a Najeriya, sun kaddamar da cibiyar ayyukan gaggawa ta yaki da yaduwar cutar zazzabin Lassa dake bazuwa a wasu sassan kasar.

Wata sanarwa da cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasar NCDC ta fitar, ta ce wannan mataki ya zama wajibi, duba da yadda ake samun karuwar cutar Lassa a Najeriya, don haka za a gudanar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin sassan hukumomin lafiya da na abokan aiki.

Cibiyar ta ce ya zuwa ranar Lahadin karshen makon jiya, an tabbatar da harbuwar mutane 115, daga kananan hukumomi 30 na jihohin kasar 11 da suka harbu da cutar, ciki har da mutum 26 da cutar ta hallaka.

Cibiyar NCDC ta kara da cewa, tana ci gaba da aiki tukuru, wajen tallafawa rukunonin jami’an lafiya na cimma burin da aka sanya gaba, don gane da rage asarar rayuka sakamakon harbuwa da cutar Lassa, da kuma karfafa kandagarki da dakile barazanar cututtuka a kasar.    (Saminu Fagam)