logo

HAUSA

MDD ta bukaci a kara azama wajen gudanar da ayyukan jin kai a Afghanistan

2022-01-27 10:51:33 CRI

MDD ta bukaci a kara azama wajen gudanar da ayyukan jin kai a Afghanistan_fororder_220127-saminu-Afghanistan

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kara azama wajen ceton rayuka, ta hanyar gudanar da ayyukan jin kai na gaggawa a Afghanistan.

Mr. Guterres wanda ke bayani game da yanayin tattalin arziki da al’ummar Afghanistan ke ciki a yanzu, ya ce jama’ar kasar na rayuwa cikin matsanancin yanayin sanyi, da kamfar ababen bukata na yau da kullum.

Ya ce ya zama wajibi a gaggauta tallafawa tattalin arzikin Afghanistan ta hanyar shigar da karin kudade, a hannu guda kuma, ya kamata kungiyar Taliban ta yi aiki kut da kut da sassan kasa da kasa, wajen dakile barazanar ’yan ta’adda ga kasar, tare da gina hukumomi daka iya inganta tsaron kasar.

Daga nan sai Mr. Guterres ya jinjinawa matakin kwamitin tsaron MDD, na tsame Afghanistan daga cikin kasashen da aka dakatar da baiwa tallafin jin kai.   (Saminu)