logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Shanxi

2022-01-27 14:16:26 CRI

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Shanxi_fororder_Xi1

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Shanxi_fororder_Xi2

 

A gabannin bikin bazara, wanda ya kasance sabuwar shekarar gargajiyar kasar Sin, babban sakataren kwamitin koli na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Xi Jinping, ya ziyarci lardin Shanxi don gudanar da rangadin aiki.

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Shanxi_fororder_Xi4

Xi Jinping ya yi rangadin aiki a lardin Shanxi_fororder_Xi3

Da yammacin jiya 26 ga wata, ya ziyarci kauyen Fengnanyuan na garin Shizhuang da ke birnin Huozhou, da kauyen Duan na garin Sengnian da ke gundumar Fenxi, inda ya je gidajen mazauna kauyukan don kara fahimtar ayyukan sake farfadowa bayan bala’u, da aikin shuke-shuke a lokacin sanyi, don tabbatar da ganin al’umma sun yi zamansu cikin tsaro yadda ya kamata a lokacin hunturu, baya ga ganin yadda ake gudanar da ayyuka, don magance komawa kangin talauci, da ma kara farfado da yankunan karkara. (Kande Gao)