logo

HAUSA

Jami’in: Gwajin COVID-19 yana tabbatar da lafiya da aminci a gasar Beijing 2022

2022-01-27 21:18:36 CRI

Jami’in: Gwajin COVID-19 yana tabbatar da lafiya da aminci a gasar Beijing 2022_fororder_微信图片_20220127211759

Masu shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na shekarar 2022 da za a bude cikin ‘yan kwanaki a birnin Beijing na kasar Sin, sun bayyana cewa, gwajin COVID-19 a lokacin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, ya dace da ka'idojin kasa da kasa kuma zai tabbatar da lafiya da amincin 'yan wasa da masu ruwa da tsaki.

Mataimakin darektan ofishin yaki da cututtuka na kwamitin shirya gasar Olympics ta Beijing Huang Chun ya bayyana cewa, aikin rigakafin a gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing ya kasance mai tsauri kuma bisa kimiyya. Haka kuma, an tabbatar da tsarin gwajin da dakunan gwaje-gwajen annobar da ake amfani da su yadda ya kamata, kuma sun dace da ka'idodin kasa da kasa.

Ya mai cewa, za mu tabbatar da cewa, ba a samu wani kuskure, idan aka zo ga bayanan gwajin COVID-19 da sakamakon ba.