logo

HAUSA

Sin: Shugaban kasar Argentina zai halarci bikin bude gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da kuma ziyartar kasar Sin

2022-01-26 21:18:18 CRI

Sin: Shugaban kasar Argentina zai halarci bikin bude gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, da kuma ziyartar kasar Sin_fororder_9d82d158ccbf6c81ccc28533a3dd123c31fa4064

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Larabar nan cewa, shugaban kasar Argentina Alberto Fernández zai halarci bikin bude gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing, zai kuma ziyarci kasar Sin daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Fabrairu. Wannan ita ce ziyarar farko da shugaba Alberto Fernández zai kai kasar Sin.