logo

HAUSA

Xi ya mika sakon taya murna ga 48 Group Club

2022-01-26 20:57:55 CRI

Xi ya mika sakon taya murnar bikin sabuwar shekara ta 2022 na kasar Sin_fororder_20181017031735126

Larabar nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga bikin sabuwar shekara ta 2022 na kasar Sin, wanda kungiyar cinikayya ta Burtaniya da ake kira 48 Group Club ta shirya a birnin London.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a cikin shekarun 1950 ne, 'yan kasuwa na Burtaniya da Mr. Jack Perry ya wakilta,suka fara "tattakin kawo karshen shingen kasuwanci tsakanin kasashen yammacin duniya da kasar Sin. A bana ake cika shekaru 50 da kulla huldar jakadanci tsakanin Sin da Birtaniya. Idan muka waiwayi baya, ba za mu manta da tsoffin abokai da suka ba da gudummawa a tarihi, wajen raya dangantakar da ke tsakanin Sin da Birtaniya ba. Idan muka kalli gaba, ina fatan masu hangen nesa da wakilan 'yan kasuwa na kasashen biyu, za su martaba “Ruhin kawo karshen wannan shinge” da ci gaba da fadada hadin gwiwar moriyar juna, da karfafa zumuncin kasar Sin da Birtaniya, da kuma kyautata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda zai amfani kasashen biyu da al'ummarsu yadda ya kamata.