logo

HAUSA

Mataimakin shugaban IOC ya ce gasar Olympics tamkar gada ce ba Katanga ba

2022-01-26 14:19:21 CRI

Mataimakin shugaban IOC ya ce gasar Olympics tamkar gada ce ba Katanga ba_fororder_220126-A3-IOC

Ng Ser Miang, mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa IOC ya ce, siyasantar da wasannin Olympic ba shi da wani alfanu sai dai ma zai iya shafar dubban ’yan wasa wadanda suka shafe shekaru masu yawa ko kuma tsawon rayuwarsu baki daya suna shirye-shiryen wasannin.

Ya kara da cewa, su kansu wasannin suna samar da damammaki ga duk duniya wajen haduwar al’umma waje guda, ba tare da la’akari da banbancin kabila, ko jinsi, ko addini ko ma banbancin shekaru ba.

A wannan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu, “Beijing ya kafa wani muhimmin tarihi, inda ya zamo birni na farko a tarihin duniya da ya karbi bakuncin dukkan gasar wasanni biyu na lokacin zafi da kuma na lokacin sanyi. (Ahmad)