logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga dandalin kirkire-kirkire a fannin kafafen yada labarai na duniya na farko

2022-01-26 21:07:56 cri

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga dandalin kirkire-kirkire a fannin kafafen yada labarai na duniya na farko_fororder_f44d305ea1af235b368447

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga dandalin yin kirkire-kirkire kan kafofin yada labarai na duniya na farko.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, taken wannan dandalin shi ne, "Raba ruhin wasannin Olympics na lokacin sanyi ta hanyar amfani da kimiyya da fasaha", yana fatan mahalarta gasar za su yi amfani da hikima, da musaya da raba kwarewa, da taimakawa wajen nuna fara'a na musamman na wasannin kankara da dusar kankara, kana da raya ruhin Olympics, tare da ciyar da wasannin Olympics na lokacin sanyi gaba.

A yau ne, aka bude dandalin kirkire-kirkire kan kafofin watsa labaru na duniya karo na farko ne a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ya karbi bakunci. (Mai fassara: Bilkisu Xin)