logo

HAUSA

Sin ta yaba sosai da irin goyon bayan da shugaba Putin ya bayar ga wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2022-01-26 21:13:32 CRI

Sin ta yaba sosai da irin goyon bayan da shugaba Putin ya bayar ga wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing_fororder_4e4a20a4462309f7073da153d08cc6fad6cad6a9

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, kasar Sin ta yaba matuka da gagarumin goyon bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya nuna ga gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar ta Rasha Vladimir Putin, ya bayyana a wani taro ta kafar bidiyo da ya yi da tawagar ‘yan wasan gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na kasarsa a jiya cewa, kasashen Rasha da Sin suna adawa da siyasantar da wasannin motsa jiki, da yadda wasu ke fakewa da wani salo don neman da kaurace wa gasar, da kuma martaba tsarin nuna daidaito da adalci a gasar Olympics. A wannan rana, jakadan kasar Rasha dake kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Rasha za ta aike da tawagar 'yan wasa masu karfi da za su halarci gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi na birnin Beijing, kuma ta yi imanin cewa, gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, za ta zama wani taron wasanni da zai gudana cikin nasara.