logo

HAUSA

Allurar rigakafi karo na biyu da Sin ta samarwa Zambiya ta isa Lusaka

2022-01-25 13:49:55 CRI

Allurar rigakafi karo na biyu da Sin ta samarwa Zambiya ta isa Lusaka_fororder_b7fa425331f3446db0546d72d61809d0

Da safiyar jiya ne allurar rigakafin cutar COVID-19 karo na biyu da Sin ta samarwa Zabiya ta isa filin jirgin sama na Kenneth Kaunda dake Lusaka babban birnin kasar, inda ministar kiwo lafiya na kasar Madam Sylvia Masebo, da jadakan Sin dake kasar Li Jie suka yi maraba da zuwan alluran a filin jirgi.

Da take jawabi, madam Sylvia Masebo ta godewa taimakon da Sin ke baiwa kasar a fannin dakile cutar, a cewarta alluran sun zo a daidai lokacin da ake neman su kamar ruwa a jallo, kuma za su taimakawa kasar wajen samun isassun alluran. Ta ce, taimakon da Sin ke baiwa kasar na kara bayyana ingancin huldar dake tsakanin kasashen biyu da ba za a iya yiwa cikas ba. Ta kuma yi alkawarin cewa, sabbin ministocin kasar za su inganta huldar sada zumunta da tsoffin shugabannin kasar suka kafa, kuma za a tsaya tsayin daka wajen ingiza hadin kan kasashen biyu a nan gaba.

A cikin jawabinsa, jadaka Li ya nuna cewa, kasashen biyu na da daddaden zumunci. Suna hadin kai tun lokacin barkewar cutar a kasar, tare da samun ci gaba mai kyau. Ya ce gwamnatin Sin za ta ci gaba da baiwa Zambiya taimako, da tallafi a nan gaba gwargwadon karfinta, tare da habaka hadin kansu a fannin magunguna da kiwo lafiya da sauransu.  (Amina Xu)