logo

HAUSA

Tawagar ‘yan wasannin kasar Sin sun yi rantsuwar shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi na shekarar 2022

2022-01-25 13:53:22 CRI

Tawagar ‘yan wasannin kasar Sin sun yi rantsuwar shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi na shekarar 2022_fororder_b21c8701a18b87d6702c386b57c8e0311e30fda6

Da safiyar yau Talata ne mambobin tawagar ‘yan wasan kasar Sin, da kocinsu, su fiye da mutum 100 suka taru a filin Tian’anmen dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar, don kallon bikin daga tutar kasar, tare da yin rantsuwar shiga gasar Olympics ta lokacin sanyi na shekarar 2022.

Wu Dajing, wani shahararren dan wasa na kasar Sin, shi ne ya jagoranci bikin. Bayan bikin rantsuwar ‘yan wasan, za su killace kan su domin shirya gasar, ta yadda za su shiga gasar bisa tsarin da aka tanada. (Amina Xu)